Trump Ya Jinkirta Karin Haraji Kan Kayakin China
(last modified Mon, 25 Feb 2019 10:10:35 GMT )
Feb 25, 2019 10:10 UTC
  • Trump Ya Jinkirta Karin Haraji Kan Kayakin China

Shugabann Amurka Donald Trump, ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewa, zai jinkirta amfani da karin haraji kan kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasarsa da aka shirya fara amfani da shi a ranar 1 ga watan Maris.

Shugaban da ya bayyana haka a jiya, ya ce zai jinkirta ne saboda tattaunawa mai ma'ana da aka yi tsakanin kasashen biyu.

Kasashen Sin da Amurka, sun samu ci gaba kan wasu batutuwa, biyo bayan tattaunawar baya-bayan nan da manyan jami'ansu suka yi, kan harkokin tattalin arziki da cinikayya da ta gudana a binin Washington.

Bisa la'akari da ci gaban da aka samu ne, bangarorin biyu za su ci gaba da aiki domin shiga sabon mataki, bisa umarnin shugabannin kasashen biyu.