Gwamnatin Venezuela Ta Kori Jakadan Jamus A Kasar
Gwamnatin Shugaba Nicolas maduro na kasar Venezuela ta sanar da korar jakadan kasar Jamus, daga kasar.
Sanarwar da gwamnatin venezuela ta fitar, ta ce an baiwa jakadan na Jamus, Daniel Kriener, wa'adin sa'o'i 48 na ya bar kasar, saboda shishigin da yake yi a cikin al'amuran cikin gidan kasar.
Jakadan na Jamus yana daga cikin jakadun kasashen waje da ke birnin Caracas wadanda kuma suka tarbi jagoran 'yan hammaya na kasar ta Venezuela, Juan Guaido, wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na riko, a filin jirgi sama na Caracas bayan ya dawo daga ziyarar da ya kai a wasu kasashen yankin.
Sanarwar dai bata fayyace ko matakin ya shafi sauren jakadun kasashen wajen da suka tarbi Mista Juan Guaidon ba.
Jakadun kasashen waje 12 ne dai suka tarbi M. Guaido a lokacin da ya dawo daga rangadin.
Mista R. Guaido ya bayyana matakin na gwamnatin Maduro da cewa barazana ce ga 'yancin walwala.