Bankin Duniya Ya Taimakawa "'Yan Rohingyas Da Dala Miliyan 165
Babban bankin duniya ya bayar da tallafin kudade da suka kai dala miliyan 165 ga 'yan gudun hijirar Rohingya da suke tsugunne a kasar Bangaladesh.
Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, babban bankin duniya ya bayar da tallafin kudade dala miliyan 165 ga 'yan gudun hijirar Rohingya da suke tsugunne a kasar Bangaladesh, domin taimaka musu.
Bayanin ya ce wadannan kudade za a yi amfani da su domin samar da abubuwan bukata ga 'yan gudun hijirar na Rohingya, da hakan ya hada da samar musu da tsaftataccen ruwan sha, da kuma gyara musu muhallin da suke zaune a sansanonin yankunan Teknaf, da kuma Ukhia Upazila da aka tsugunnar da su.
Bisa rahoton majalisar dinkin duniya ya zuwa yanzu akwai fiye da 'yan gudun hijira 'yan kabilar Rohingya dubu 750 a cikin kasar Bangaladash.