Faransa: An karfafa Matakan Tsaro A Wuraren Ibadu.
Ministan cikin gidan kasar Faransa ya bukaci sa ido da karfafa matakan tsaro a wuraren ibadu na fadin kasar gaba daya, bayan harin ta'addancin da aka kai masallatai biyu a kasar New-Zeland.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Christophe Castaner ministan harakokin cikin gidan kasar Faransa a wannan juma'a na bayyana alhinin al'ummar kasar Faransa ga al'ummar kasar New-Zeland dangane da harin ta'addancin da aka kai a masallatai na yankin Christchurch, sanan ya bukaci jami'an tsaron kasarsa da su sanya ido da kuma karfafa matakan tsaro a wuraren ibadu na fadin kasar baki daya.
Bayan kai harin ta'addancin na kasar New-Zeland, jami'an 'yan sandar kasar sun sanar da kame mutum 4 da ake zarkin su nada hanu a harin.
Firai ministan kasar New-Zeland Jacinda Ardern ya bayyana cewa mutune hudun da aka kama nada alaka da wasu kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi, amma ba su kasance cikin sanya idon jami'an leken asirin kasar ba.