Mar 20, 2019 14:43 UTC
  • Faransa : Za'a Jibge Sojoji Don Tunkarar Masu Bore

Hukumomi a Faransa, sun ce za'a tsaurara matakan tsaro ta hanyar jibge sojoji na tawagar yaki da ta'addanci domin tunkarar masu zanga zanga da akewa lakabi da masu ''dorawa riga'' a ranar Asabar mai zuwa.

Hakan a cewar hukumomin kasar nada nufin kare gine gine na gwamnati da kuma wasu wurare masu mahimmanci, kamar yadda wata sanarwar gwamnatin aksar ta sanar a yau Laraba.

Da yake sanar da hakan kakakin gwamnatin kasar, Benjamin Griveaux, ya ce wannan matakin da shugaban kasar Emmanuel Macron, ya dauka, zai baiwa jami'an tsaro damar sanya ido sosai kan masu boren, domin tabbatar da doka da oda.

Wannan matakin dai na zuwa ne kwana hudu bayan mummunar zanga zangar da masu dorawar rigar sukayi a ranar Asabar data gabata, a babban tinin Champs-Elysées, inda suka kona shaguna da kwasar ganima da kuma lalata wurare da dama, baya ga artabu tsakaninsu da jami'an tsaro.

A ranar Asabar data gabata aka shiga mako na 18 na boren, da jama'ar kasar keyi na kin jinin manufofin gwamnatin shugaba Macron, musamman kan batun haraji da ci gaba da yin burus da bukatun masu karamin hali.

Tags