Holland ya rasa goyon bayan jam'iyarsa a zaben 2017
Jamiyar 'yan gurguzu ta kasar Faransa ta bayyana adawarta da tsayawa takarar shugaban kasar mai Francois Holland
A wani Rahoto da ta fitar jiya, jam'iyar 'yan gurguzu ta kasar Faransa ta babbana ta shiryawa zaben shugaban kasa na 2017 saidai babu yadda za a yi ta goyin bayan takarar shugaba Francois Holland, kuma jam'iyar ta ce za ta fitar da 'yan takarar da zai magance matsalar 'yan kasar.
A bangare guda Farin jinin shugaba Hollande na ci gaba da raguwa sosai a tsakanin al’ummar kasar, domin yawan ‘yan kasar da suka ware lokacinsu domin sauraran zantawar da ya yi tare da ‘yan jarida a jiya bai taka kara ya karya ba.
Shugaba kasar ta Faransa Francois Hollande dake ta kokarin sake dawo da martabar sa a jiya alhamis ya bayyana a tashar talabijen na Canal France 2 na kasar domin amsa tambayoyin manema labarai.
Yayi da rage shekara guda kacal a gudanar da babban zaben kasar Faransa ,Francois Hollande na sa ran gani yan kasar sun bashi goyan bayan da ya dace domin sake samun wani sabon wa'adi na biyu a babban zabe na shekara ta 2017.