Ausrralia na adawa da karbar 'yan gudun hijra a kasashen Turai
https://parstoday.ir/ha/news/world-i430-ausrralia_na_adawa_da_karbar_'yan_gudun_hijra_a_kasashen_turai
Ministan Kudi na kasar Australia ya ce kwararen 'yan gudun hijra zuwa kasashen Turai shine musababin fuskantar matsalar gudi.
(last modified 2018-08-22T06:57:46+00:00 )
Feb 07, 2016 08:29 UTC
  • Ausrralia na adawa da karbar 'yan gudun hijra a kasashen Turai

Ministan Kudi na kasar Australia ya ce kwararen 'yan gudun hijra zuwa kasashen Turai shine musababin fuskantar matsalar gudi.

A wata wasika da ya aikewa shugaban kwamitin dake kula da 'yan gudun hijra na kungiyar Tarayyar Turai , Ministan Kudin kasar Australia Mista Hans-Joerg Schelling ya bayyana cewa ya zuwa yanzu kasashen Turai ba su fuskanci wata matsala mai sarkakiya da suka kasa cimma matsaya ba, kamar matsalar kwararen 'yan gudun hijra a wannan lokaci.

Mista Schelling ya kara da cewa idan 'yan gudun hijrar suka ci gaba da kwarara cikin turain, gwamnotocin kasashen za su dauki nauyin kara yawan kudaden da suke samarwa domin biyan bukatun 'yan gudun hijrar, kuma idan aka kasa magance matsalar kwararen 'yan gudun hijrar ba, to babu shakka kasashen turai za su fuskanci matsalar gudi a nan gaba.

A wata sanarwa da ta fitar Gwamnatin Austrelia ta bayyana cewa nan da shekaru uku masu zuwa za ta kori 'yan gudun hijra kimanin dubu 50.