Shugaba Holland ya soki wadanda suka sanya wuta a massalacin Musulmai
Shugaban Kasar Faransa Fransois Holland ya ce ba za su amince da duk wani yunkuri na kai hari ga wani Addini a kasar ba
Jaridar Le figaro ta kasar Faransa ta nakalto Francois Holland shugaban kasar cikin wani bayyani da ya fitar a Yau Assabar na cewa ba za su amince da duk wani hari da za a kaiwa mabiya wani addini a kasar ba, kuma wadanda suka sanya wutar a Massalacin matukar bincike ya nuna cewa da gamgam ne za a gurfanar da su a gaban kuliya.
Francois Holland ya bayyana cewa Al'ummar kasar su mabiya Addinin Islama dake zauce a tsibirin Kurs suna aiki kafada da kafada tare da jami'an tsaro domin kare kasar.
A jiya Juma'a ne wasu Mutane da ba a san ko su waye ba, suka sanya wuta A massalacin Al'ummar musulmuin garin Ajakiso dake tsirin Kours na kasar Faransa.
Wannan wuta ta yi sanadiyar asarar mai dunbun yawa a wannan massalacin.