Ministocin Harkokin Wajen Faransa Da Jamus Na Ziyara A Nijer
https://parstoday.ir/ha/news/world-i4735-ministocin_harkokin_wajen_faransa_da_jamus_na_ziyara_a_nijer
Ministocin harkokin wajen Faransa da Jamus na gudanar da wata ziyara aiki a jamhuriya domin tattaunawa da mahukuntan kasar kan batutuwan da suka shafi matsalar kwararen bakin haure da kuma tsaro a yankin Sahel.
(last modified 2018-08-22T06:58:13+00:00 )
May 03, 2016 13:24 UTC
  • Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault da takwaransa na Jamus Frank-Walter Steinmeier
    Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault da takwaransa na Jamus Frank-Walter Steinmeier

Ministocin harkokin wajen Faransa da Jamus na gudanar da wata ziyara aiki a jamhuriya domin tattaunawa da mahukuntan kasar kan batutuwan da suka shafi matsalar kwararen bakin haure da kuma tsaro a yankin Sahel.

A wannan Talata an shirya Mr Jean-Marc Ayrault na Faransa da takwaransa na Jamus Frank-Walter Steinmeier, zasu gana da shugaban kasar ta Nijar Alh. Mahamadou Issoufou, kafin su gana da wasu bakin haure da suka dawo daga kasashen Aljeriya da Libya.

Kafin Nijar dai ministocin biyu sun gudanar da irin wannan ziyara a kasar Mali.

Nijar na daga cikin kasashen dake fuskantar matsalar tsaro dake da nasaba da Boko haram a yankin kudu maso gabashin ta, ga kuma matsalar 'yan tada kayar baya dake kan iyakar ta da Mali, ga kuma 'yan ta'ada da masu fataucin miyagun kwayoyi a arewacin ta dake iyaka da kasar Libya, wanda yasa take da mahimanci a duk wani mataki na kokarin dakile miyagun ayyukan a yankin na Sahel.

Kazalika Kasar Nijar dake yammacin Afirka na zaman wata mashiga ta bakin hauren Afirka dake neman shiga kasashen larabawa na Magreb inda daga cen wasunsu ke tsallakawa ta teku zuwa Turai da zumar samun ingantacen rayiwa.