Kare Asibitoci da Ma'aikatan Kiwan Lafiya A Lokutan Yaki
kwamitin tsaro na MDD ya amunce da wani kudiri a yau Talata da zai kara himma wajen kare asibitoci da ma'aikatan kiwan lafiya a lokutan rikici-rikice.
kwamitin ya dau wannan matakin ne, duba da yadda farmaki kan asibitoci ke son zama ruwa dare gama duniya a kasashen Syria, Yemen da kuma Afganistan.
kwamitin ya ce ire-iren wadanan laifukan zasu iya zama laifikan yaki.
kungiyar agajin gaggawa ta kasa da kasa ta Médecins sans frontières (MSF) ta bukaci kwamitin daya aiwattar da wannan kudirin a matakin ba sani ba sabo, tare da mika bukatarsa ga kasashe membobin kwamitin na dindin-din da suka hada da Amurka, Rasha, Faransa, da Biritaniya da China su bada misali akan wannan kudiri.
kungiyar ta zayyano dakarun wasu kasasshen duniya da suka aikata irin wadanan dayan ayyukan musamen irin na NATO a Afganistan da kuma kawacen da Saudiyya ke jagoranta a kasar Yemen.