Matasan Kasar Congo Brazzaville Suna Nuna Damuwa Kan Cin Zarafinsu
(last modified Thu, 05 May 2016 17:05:01 GMT )
May 05, 2016 17:05 UTC
  • Matasan Kasar Congo Brazzaville Suna Nuna Damuwa Kan Cin Zarafinsu

Matasa a birnin Brazzaville fadar mulkin kasar Congo sun fara nuna damuwa kan yadda jami'an tsaron kasar ke ci gaba da musguna musu tun bayan kai harin ranar 4 ga watan Aprilun da ya gabata a birnin na Brazziville.

Matasa a birnin Brazzaville fadar mulkin kasar Congo sun bukaci mahukuntan kasar da su dauki matakin kiyaye tsarin dokar kame mutanen da ake zargi da aika laifi a kasar tare da mutunta hakkin bil-Adama. Wannan koke na matasa a birnin Brazzaville ya zo ne sakamakon yadda jami'an 'yan sandan kasar ke ci gaba da kame matasa a duk lokacin da suka ga dama musamman ta hanyar kai farmaki kan wajajen taruwar matasa a birnin ba dare ba rana.

Matasar birnin na Brazzaville sun koka da cewa; Matashi baya da hakkin fitowa kan hanya ko zuwa wajen shakatawa, sakamakon masifar awungaba da matasa a jami'an tsaron kasar ke yi kullum rana.

Majiyar rundunar 'yan sandan Congo Brazzaville ta bayyana cewa; Samamen da jami'an tsaron kasar ke kai wa yana daga cikin hanyoyin zakulo 'yan ta'adda ne a birnin.