An kori wata Daliba musulma daga Makaranta a Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i4981-an_kori_wata_daliba_musulma_daga_makaranta_a_faransa
An kori wata Daliba musulma daga Makaranta saboda ta sanya dogon hijabi a kasar Faransa
(last modified 2018-08-22T06:58:15+00:00 )
May 09, 2016 05:52 UTC
  • An kori wata Daliba musulma daga Makaranta a Faransa

An kori wata Daliba musulma daga Makaranta saboda ta sanya dogon hijabi a kasar Faransa

Daraktan wannan makaranta dake gefen birnin Paris ya shaidawa Dalibar mai shekaru 16 a Duniya, wannan hijabi da ta sanya yana nufin wata alama ta Addini, kuma bisa dokar kasar ta shekara 2014 an haramta amfani da wata alama ta addini a makarantun Gwamnatin kasar.

Bisa dokar kasar Faransa duk wasu kaya da mutum zai sanya ko da dogaye ne babu laifi matukar ba wata alama ba ce ta wani addini.

Ita dai wannan daliba 'yar kasar Portigal ta karfi Addinin islama ne a shekarar 2015 da ta gabata kuma ta gudanar da bincike dangane da alakar yanayin karantarwar Faransa da Addinin Islama.

A shekarar 2004, Gwamnatin kasar Faransa ta haramtawa dukkanicin dalibai musulmai sanya hijabi a cikin Makarantun Gwamnati.