Taho mu gama tsakanin 'yan sandar Faransa da masu zanga-zanga
Kudiri da Gwamnatin Faransa ta dauka na gudanar da gyara ga dokokin Ma'aikata ba tare da amincewar Majalisar Dokokin kasar ba ya janyo zanga-zanga a kasar
Tashar telbijin din Press TV ta habarta cewa Dariruwan Ma'aikatan kasar Faransa suka tsuntsurundo a gaban Majalisar Dokokin kasar domin nuna adawarsu da kudirin da gwamnatin ke son dauka na gudanar da sauye sauye a kundin dokokin Ma'aikatan kasar, inda saida Jami'an 'yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sanya hawaye domin tarwatsa mahalarta zanga-zangar.
A Wasu Gariruwan kudancin kasar ma an gudanar da irin wannan zanga-zanga, inda jami'an 'yan sanda suka yi amfani da barkonan tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar
Gwamnatin Faransa ta kare kanta kan kudirin da take son dauka, inda ta ce wannan shi zai sanya Gwamnati ta kara yawan ma'aikatan da take da su kuma a rage yawan marassa aikin yi, saidai a na su bangare, kungiyoyin kwadago na ma'aikata da na dalibai sun bayyana cewa wannan kudiri zai sanya duban ma'aikatan da ake so kora a wasu kamfanonin kasar sun shiga cikin mawuyacin hali na kudi da rashin aikin yi.
Rahoton ya ce wannan gyara da shugaban kasar ta Faransa ke son yi zai samarwar marassa aiki yi da dama aiki, amma duk da haka yana shan kakkausar suka daga kungiyoyin kwadago na Ma'aikatan kasar,
Har ila yau an bayyana cewa Shugaba Holland zai halarci wata gagarumar zanga-zanga da kungiyoyin kwadago 7 tare da kungiyoyin Matasa suka shirya gobe Alkhamis a birnin Paris.