Kungiyar Unesco Ta soki Haramtacciyar Kasar Isra'ila.
Kungiyar da ke kare al'adu ta majalisar dinkin duniya ta soki yadda 'yan Sahayoniya ke kai wa yaran palasdinawa hari.
Tashar telbijin din al'alam mai watsa shirye-shiryenta daga nan Tehran da larabci ta ambato kungiyar ta Unesco wacce ke kula da kare al'adu da kuma ilimantarwa na fitar da wani bayani a yau asabar da a ciki ta nuna rashin dadinta akan yadda 'yan sahayoniyar ke kai wa kananan yaran palasdinawa hari.
A gefe daya shi ma Asusun kananan yara na majalsiar dinkin duniya Unicef ya bayyana nashi rashin jin dadin da damuwa akan cin zarafin yaran palasdinawa da 'yan sahayoniyar su ke yi.
Bayanin ya kunshi cewa a cikin watannin Oktoba da nuwamba da Decemba na 2015 kadai, sojojin Sahayoniya sun kashe kananan yaran palasdinawa biyar da kuma jikkata wasu 1310.