Damuwar MDD kan yadda rikicin kasar Burundi ke kara kamari
Majalisar Dinkin Dunmiya ta bayyana Damuwarta kan yadda rikici a kasar Burundi ke kara kamari.
A yayin da yake bayyani kan yadda rikici ke kara tsanani tare da yawan kame-kame a kasar Burundi gami da jan hankalin Gwamnati, Kakakin MDD Farhan Haq a jiya Litinin ya bayyana cewa tsanantar rikicin ba ya rasa nasaba da kusantarwar zagayewar shekarar farko na kokarin da aka yi na yiwa Shugaban kasar mai ci Pierre Nkurinziza juyin milki.
Kakakin MDD ya ce har yanzu suna sake kiran Gwamnatin ta Burundi da bangaren 'yan adawa su zauna kan tebirin tattaunawa domin kawo karshen rikicin siyasar da kasar ke fama da shi.
Kimanin Mutane 100 aka kame ranar Juma'a da ta gabata a yankin Musaga dake kudancin Bujunbura babban birnin kasar,baya ga haka, Jami'an tsaron kasar sun tsananta kame-kame a karshen Makun da ya gabata.
Daga cikin mutane kusan Darin da aka kame na yankin Musaga rahotanni sun bayyana cewa an sako da dama daga cikin su.
Tun a watan Avrilun shekarar 2015 din da ya gabata ne kasar Burundi ta fada cikin rikicin siyasa bayan da Shugaba N'kurinziza ya bayyana aniyarsa na tsayawa takarar shugasbancin kasar karo na uku, lamarin da ya yi sanadiyar lashe rayukan mutane sama da 500 sannan kuma ya raba wasu kimanin dubu 270 da mahalinsu.