Jirgin Egypt Air Ya Fadi Ne A Tekun Bahar Rum
https://parstoday.ir/ha/news/world-i5380-jirgin_egypt_air_ya_fadi_ne_a_tekun_bahar_rum
Rahotanni dake cin karo da juna na cewa jirgin fasinja nan na Egypt Air daya taso daga Paris zuwa Alkahira ya fadi ne a tekun Bahar Rum.
(last modified 2018-08-22T06:58:17+00:00 )
May 19, 2016 06:41 UTC
  • Jirgin Egypt Air Ya Fadi Ne A Tekun Bahar Rum

Rahotanni dake cin karo da juna na cewa jirgin fasinja nan na Egypt Air daya taso daga Paris zuwa Alkahira ya fadi ne a tekun Bahar Rum.

koda yake kawo yanzu ba'a bayyana musababin faduwar jirgin ba, aman bayanai sun nuna cewa ya rikito a gaf da tsibirin Karpathos dake kudancin Girka a daidai lokacin ya shiga sararin samaniyar kasar Masar.

Jirgin kirar Airbus A 320 wanda ya bar filin jirgin saman Paris na faransa a cikin daren jiya Laraba na daukeda mutane 66, da suka hada da faransawa 15 da 'yan Masar 30, kuma an bar jin duriyarsa ne mil biyar kafin ya shiga sararin samaniyar kasar ta Masar.