An Gano Tarkacen Jirgin EgyptAir
May 20, 2016 05:08 UTC
Rundinar sojin kasar ta sanar da gano takarcen jirgin saman EgyptAir wanda ya fada a tekun Bahar Rum da jijibin safiyar Alhamis.
Jirgin kirar Airbus A320 wanda ya taso daga filin jirgin saman Charl de Gaul a Paris zuwa birnin Alkahira cikin daren Laraba data gabata daukeda fasinjoji 66 da kuma ma'aikatansa, kafin daga bisani ya bata.
bayan sanar da faduwar jirgin ne aka kaddamar da gagarumin bincike domin yiwuwar gano jirgin da yayi batan dabo a kusa da tsibirin Karpathos da ke Girka.
Tags