Amurka Ta Kafa Wa Pakistan Sharudda Kafin Ba Ta Taimakon Kudade
(last modified Sat, 21 May 2016 05:11:46 GMT )
May 21, 2016 05:11 UTC
  • Amurka Ta Kafa Wa Pakistan Sharudda Kafin Ba Ta Taimakon Kudade

'Yan majalisar wakilan Amurka sun sanar da wasu sabbin sharuddan da wajibi ne gwamnatin Pakistan ta cika su kafin su amince gwamnatin Amurka ta ba ta kudaden taimakon da ta sa ba ba ta.

Rahotanni daga Amurkan sun ce wasu 'yan majalisar wakilan Amurka su 277 sun bayyana rashin amincewarsu da ba wa gwamnatin Pakistan taimakon kudi dala miliyan 450 da gwamnatin Amurka take shirin yi har sai gwamnatin ta Pakistan ta cika wasu sharudda guda uku da suka gindaya mata.

Sharuddan dai sun hada da cewa wajibi ne gwamnatin Pakistan din ta kawar da kungiyar 'yan ta'addan nan ta Haqqani da ke kasar wadanda gwamnatin Amurkan take ganinsu a matsayin barazana ga sojojinta da suke kasar Afghanistan. Sharadi na biyu kuma shi ne cewa gwamnatin ba za ta yi amfani da dukiya da sauran kayayyakin taimakon da za a ba ta din wajen matsin lamba ga kungiyoyi da kabilu 'yan tsirarru na kasar ba, sai kuma sharadi na uku wanda shi ne wajibi ne gwamnatin Pakistan din ta sake wani likita dan kasar mai suna Shakeel Afridi wanda gwamnatin ta Pakistan take tsare da shi bisa zargin aiki wa hukumar leken asirin Amurka CIA, wanda kuma shi ne ya taimaka wa Amurka da bayani kan Usama bin Ladin da ya kai ma gano inda ya ke a Pakistan din har sojojin Amurka suka kashe shi.

Cikin 'yan watannin baya-bayan nan dai alaka tsakanin Pakistan da Amurka ta yi tsami sakamakon kin amincewar Amurkan na ba wa Pakistan din taimakon kudaden da suke bata bugu da kari kan matsin lambar da gwamnatin take fuskanta a cikin gida dangane da irin mika kai ga Amurkan da gwamnatin take yi.