Taron Duniya Kan Makomar 'Yan Gudun Hijira da bakin Haure
(last modified Mon, 23 May 2016 05:53:59 GMT )
May 23, 2016 05:53 UTC
  • Taron duniya kan makomar \'yan gudun hijira da bakin haure a Turkiyya
    Taron duniya kan makomar \'yan gudun hijira da bakin haure a Turkiyya

Taron wanda shi ne irin sa na farko da aka soma jiya a birnin Santambul na kasar Turkiyya na da zumar fitar da hanyoyi na bai daya domin inganta yadda ake ba da agaji da kuma yadda kasashen duniya za su ba da gudummawa dan tallafawa 'yan gudun hijira da bakin haure.

Wani rahoto da MDD ta fitar gabanin wannan taro ya nuna cewa akwai 'yan gudun hijira da bakin haure kimanin miliyan 60 a duniya, wanda rabin su sun kasance yara ne, kana kimanin wasu mutane miliyan 225 ne suka bar kasashen su da zubar zuwa wata kasa don samun ingantacciyar rayuwa.

Rahoto da mdd ta fitar ya ce Kasar Yemen ce ta farko a yawan 'yan gudun hijrar, sai Syria, sai kuma Iraqi da Ukraine sannan kuma Najeriya ta biyar.

Kasar Yemen ita ce ta farko a yawan 'yan gudun hijrar, sai kuma Syria da ta biye mata,sai Iraqi da Ukraine sannan kuma Najeriya ta biyar inji majalisar dinkin duniya.

A bayanin da mashawarciya mdd Mme AbuZayd ta yi ta ce duk wadanan mutanen na barin kasashen ne ba wai don son ran su, suna yin hakan ne saboda halin kunci da bala'in rikice-rikice da yake-yake da talauci da yake addabi kasashen su.

kuma a cewar ta babban abun damuwa a yanzu shi ne yadda yawan 'yan gudun hijira da bakin haure ke dada karuwa.

wannan kuma a cewar nada cikin batutuwan da taron zai maida hankali akan su, domin shawo kan wannan matsala.

Mme AbuZayd ta kara da cewa suna da fatan ganin wannan taron ya kara fadakar da al'umma, kuma suna fatan jama'a zasu daukan batun da muhimmanci tare da kira ga gwamnatocinsu su dauki kwararen matakai wanda zasu gabatar a taron mdd kan kwararar bakinhauren da 'yan gudun hijira da za'a yi nan gaba a ranar 19 ga watan Satumba a zauren mdd dake birnin New York.

Don haka a cewar ta wannan taro na Santambul tamakar share shagen taron koli ne na watan Satumba a New York inda za'a gabatar da dukkan shawarwarin karshen wannan taron , inda take fatan samun cikakun bayanai daga jagororin kasashen duniya wanda zasu zamo mafita ta shawo kan matsalolin kwararar bakin haure da 'yan gudun hijira.

Mdd dai na son kasashen da ke zamen hanya ga bakin haure da kuma wadanda ke karbar 'yan gudun hijira su taimakawa wadanan mutanen da hanyoyin da zasu samu karbuwa cikin jama'a, koyen harsunan kasashen su samar masu da ayyukan yi tare kuma da samun ilimi.