Ministan Harkokin Wajen Kasar Faransa Zai Yi Murabus Daga Mukaminsa
Ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius ya sanar da cewa zai yi murabus daga mukaminsa da barin gwamnatin kasar, lamarin da ke tabbatar da jita-jitan da aka jima ana yadawa na cewa zai yi murabus din.
Ministan harkokin wajen na Faransa yasanar da hakan ne a yau din nan Laraba inda ake sa ran zai halarci taron majalisar ministocin kasar na karshe a matsayinsa na ministan harkokin waje.
Wasu rahotannin sun ce shugaban kasar Faransan Francois Hollande zai nada shi a matsayin shugaban babbar kotun tsarin mulki na kasar bayan ya bar ma'aikatar harkokin wajen.
Wannan lamarin dai ya zo ne kwana guda bayan da 'yan majalisar kasar suka kada kuri'a da kyar ta amincewa da yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar don tube wa mutanen da aka same su da laifin ta'addancin rigar 'yan kasa, lamarin da ya sanya a kwanakin baya ministar shari'ar kasar Faransan Christiane Taubira yin murabus daga mukaminta.