MDD Ta Yi Maraba Da Tattaunawar Siyasa A Burundi
MDD tayi maraba da tattaunawar siyasa da aka yi a kwanan baya a birnin Arusha dake arewacin kasar Tanzania kan rikicin siyasa kasar Burundi daya ki yaki cinyewa.
Wata sanarwa da babban sakataren mdd Ban ki moon ya fitar ta yayun kakakin sa, ta jaddada cewa, yin shawarwari dake kunshe da bangarori daban daban ita ce hanya daya tak da za ta iya warware rikicin siyasa da Burundi take fuskanta.
A ranakun 21 zuwa 24 ga watan nan ne aka gudanar da tattaunawar siyasar kan rikicin Burundi, a shiga tsakanin kungiyar EAC, karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Tanzania Benjamin Nkapa, koda yake 'yan adawa na kasar basu halarci tattaunawar ba.
Aman duk da hakann Mr Nkapa ya ce, zaiyi kokarin ganawa da bangarorin da ba su halarci tattaunawar ba domin ganin sun shiga sabon zagayen tattaunawa nan gaba.
Wannan matakin dai a cewar kuma MDD abun yabawa ne sosai, ta la'akari da yadda ake kokarin warware rikicin kasar ta hanyar Lumana inji Ban Ki-Moon.
kasar Burundi dai ta fada cikin rikici ne tun bayan da shugaban kasar Pierre Nkurinziza ya bayyana anniyarsa ta tsayawa takara a karo na uku, lamarin da baiyi wa wasu jama'ar kasar dadi ba, inda tun lokacin ne har zuwa darewarsa karagar mulki a watan Yuli kasar ke fama da tashen tashen hankula da zanga-zanga.
Alkalumen da Mdd ta fitar sun nuna cewa sama da mutane 500 ne suka rasa rayukan su, kana wasu sama da 270,000 suka bar gidajen su saboda rikicin kasar.