An zabi sabon Ministan harakokin wajen kasar Faransa
An nada tsohon Piraministan kasar Faransa a matsayin sabon ministan harakokin wajen kasar
A yau ne aka nada mista Jean-Marc Ayrault tsohon Piraministan kasar a matsayin wanda ya gaji Lauren Fabuis minstan hakarokin wajen kasar da ya yi murabus a jiya Laraba.
shidai Laurent Fabius ya yi murabus daga mukaminsa bayan shafe shekaru sama da 30 ana dama wa da shi a fagen siyasar kasar yayin da ya rike mukamin Firaminista yana dan shekaru 34 da haihuwa.
Laurent Fabius dai ya kasance Ministan harakokin wajen Faransa da ake ganin ya fi fice a kasar.
Tun a 2012 ya ke rike da mukamin Ministan harakokin waje kuma a ta fuskar diflomasiya a zamaninsa, ya taka rawa wajen cimma yarjejeniyar nukiliyar Iran tare da kokarin sasanta rikicin Syria da jagorantar tattaunar barazanar ta’addanci a Afrika inda Faransa ta tura dakarunta domin wanzar da zaman lafiya.
A nasa bangare sabon Ministan harakokin wajen ya kasance Piraministan kasar tun daga ranar 15 ga watan Mayun shekarar 2012 zuwa 31 ga watan Maris din shekarar da ta gabata, bayan da ya kwashe shekaru 12 a matsayin magajin garin Nantes.
A nasa waje, Mista Laurent Fabuis Bayan sanar da ficewarsa daga gwamnatin kasar a jiya Laraba, shugaba Hollande ya ma shi tayin zama shugaban kotun kundin tsarin mulki saboda tasirin shi ga siyasar kasar, amma ya ce sai a watan Maris zai karbi aikin idan al'amuransa sun daidaita.
Ana dai ganin nan gaba Fabius zai shiga takarar shugabancin Faransa wanda zai gaji Fancios Hollande.