HKI ta hana tawagar kungiyar Tarayyar Turai shiga cikin Gaza
Magabatan HKI sun hana tawagar Majalisar kungiyar Tarayyar Turai shiga cikin zirin Gaza
Tawagar Majalisar kungiyar Tarayyar Turai ta je ne domin gudanar da bincike dangane da abinda hare-haren ta'addancin da haramcecciyar kasar Isra'ila ta kai zirin na Gaza a shekara ta 2014 ya aifar.
A wata sanarwar da tawagar da ta fitar yau ta ce magabatan haramcecciyar kasar Isra'ilan ta hana su shiga ba tareda sun basu wani dalili ba.
A cewar Martina Anderson shugabar tawagar mai gumshe da mutane 7, hanin da magabatan Isra'ilan suka yi musu, abu ne da ba za a amince da shi ba.
Martina Anderson ta kara da cewa tun daga shekarar 2011 zuwa yanzu magabatan haramcecciyar kasar Isra'ilan ba su bawa Majalisar Turan izini shiga zirin Gaza ba domin gudanar da bincike.
A harin ta'addancin da Haramcecciyar kasar Isra'ila na kaiwa Al'ummar zirin Gaza na Palastinu a watan Yunin shekara 2014, Akalla Palastinawa 2200 ne suka yi shahada.