Barack Obama: Musulmi Ba 'Yan Ta'adda Ba Ne
(last modified Wed, 15 Jun 2016 05:52:05 GMT )
Jun 15, 2016 05:52 UTC
  • Barack Obama: Musulmi Ba 'Yan Ta'adda Ba Ne

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya caccaki dan takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, dangane da kamalansa a kan harin Orlando.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Barack Obama ya mayar wa Trump da martani kan cewa, abin da ya faru na kai hari a Orlando ba dalili ba ne na kiran dukkanin musulmi 'yan ta'adda, ko kuma yin kira da a hana musulmi shiga Amurka kamar yadda Donald Trump ke yin kira.

Obama ya ce addinin musulunci ba addinin ta'addanci ba ne, kuma 'yan ta'adda ba suna wakiltar sauran musulmi ba ne, a kan haka dora alhakin abin da wasu 'yan ta'adda ke yi a kan dukkanin musulmi ba adalci ba ne, kuma Amurka kasa ce da tsarinta ke girma a akida da addini kowa.