An Gano Wasu Tarkacen Jirgin EgyptAir
An sake gano wasu daga cikin tarkacen jirgin nan na EgyptAir daya nutse a tekun Bahar-Rum a ranar 19 ga watan Jiya kamar yadda masu binciken musababin faduwar jirgin suka sanar.
Masu binciken dai sun ce an gano tarkacen jirgin da suka hada da bangaren wurin zama da matukan jirgin da kuma na fasinjoji.
Wannan dai na zuwa a daidai lokacin ake ci gaba da matsa kaimi wajen neman akwatinan nadar bayannan tukin jirgin wadanda zasu daina fitar da alamun jin duriyarsu a ranar 24 ga watan nan.
Samun akwatinan nadar bayanan tukin jirgin ne kawai zasu iya taimaka wajen gano musababbin faduwar jirgin na EgyptAir daya nutse a gabar ruwan arewacin Masar bayan ya taso daga Birnin Paris na faransa, ya kuma fadi ne bayan daina jin duriyarsa daukeda fasinjojin da matukansa su 66, wadanda duk sun mutu a hadarin.