An Gano Dukkan Akwatinan Nadar Bayannan Tukin Jirgin EgyptAir
https://parstoday.ir/ha/news/world-i6883-an_gano_dukkan_akwatinan_nadar_bayannan_tukin_jirgin_egyptair
Kwamitin dake gudanar da bincike kan musababbin faduwar jirgin Egypt Air ya sanar da gano dukkan akwatinan nadar bayyanan tukin jirgin daya nutse a tekun Bahar-Rum a watan Jiya.
(last modified 2018-08-22T06:58:27+00:00 )
Jun 18, 2016 01:20 UTC
  • An Gano Dukkan Akwatinan Nadar Bayannan Tukin Jirgin EgyptAir

Kwamitin dake gudanar da bincike kan musababbin faduwar jirgin Egypt Air ya sanar da gano dukkan akwatinan nadar bayyanan tukin jirgin daya nutse a tekun Bahar-Rum a watan Jiya.

An dai gano akwatin nadar bayanan na biyu a jiya Juma'a.

Dama kafin hakan kwamitin ya sanar da gano akwatin na farko tun a ranar Alhamis,

masu binciken sun ce an fitar da akwatin nadar bayanan wanda yayi raga-raga, aman anyi nasara fitar da bangaren akwatin dake ajiye bayanan, wanda shi ne mafi mahimmanci.

Samun wadanan akwatinan biyuz ai taimaka kwamitin binciken sanin hakikanin abunda ya faru ga jirgin, duk da cewa binciken zai dauki lokaci.

A ranar Alhamis data gabata ne hukumomin kasar masar suka sanar da gano wasu daga cikin tarkacen jirgin da ya yi hatsari a ranar 19 ga watan Mayu daya gabata a tekun Mediterranean dauke da mutane 66 bayan tashin sa daga Paris zuwa birnin Alkahira.