Ganawa A Tsakanin Ministan Harkokin Wajen Iran da Shugaban Kasar Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i7138-ganawa_a_tsakanin_ministan_harkokin_wajen_iran_da_shugaban_kasar_faransa
Muhammad Jawad Zarif Ya Gana Da Shugaban Faransa Fransua Hollande
(last modified 2018-08-22T06:58:29+00:00 )
Jun 23, 2016 13:45 UTC
  • Ganawa A Tsakanin Ministan Harkokin Wajen Iran da Shugaban Kasar Faransa

Muhammad Jawad Zarif Ya Gana Da Shugaban Faransa Fransua Hollande

Ministan harkokin Wajen Iran da ya ke ziyarar aiki a kasar Faransa ya gana da shugaban kasar Fransua Hollande a yau alhamis, idan su ka tattauna ci gaban da alakar kasashen biyu ta ke samu.

Ziyarar da Ministan harkokin Wajen kasar ta Iran ya kai faransa tana a matsayin share fagen ziyarar da shugaba Hassan Rauhani zai kai ne a nan gaba.

Zarif ya bayyana karuwar tuntubar juna da ake yi a tsakanin kasashen biyu wanda zai taimaka wajen bunkasa tsaro da zaman lafiya a cikin yankin gabas ta tsakiya.

A nashi gefen shugaban kasar Faransa ya jaddada muhimmancin bubkasa alaka a tsakanin kasashen biyu ta fuskoki da dama.