Biritaniya Ta Fice Daga Cikin Kungiyar (EU)
Jun 24, 2016 02:01 UTC
Al'ummar Biritaniya sun zabi ficewa daga cikin kungiyar tarayyar turai ta (EU)
Zaben raba gardama na jiya Alhamis na yanke shawarar ko Biritaniya za ta fice ko kuma za ta zauna cikin kungiyar ya nuna cewa kasar tayi ban kwana kungiyar ta EU.
Sakamakon kuri'a zaben ya nuna cewa wadanda ke goyan bayan ficewar kasar cikin (EU) sun samu kashi 52% na yawan kuri'un da aka kada.
A cewar rahotanni zaben ya samu karbuwa sosai daga jama'ar kasar inda aka samu kashi 72% na wadanda suka kada kuri'a.
A halin da ake ciki dai yanzu tattalin arzikin Biritaniya ya shiga rashin tabas, yayin da kuma janyewar kasar cikin kungiyar ta EU ya soma tasiri kan kudade a duniya.
Tags