Turai: Matsain Lamba Akan David Cameroon Saboda Ficewa Daga Turai:
Kiran Tarayyar Turai Ga Birtaniya Akan Gaggauta Bankwana da ita.
Tarayyar Turai ta kira yi David Cameronn na Birtaniya da ya gaggauta bude tattaunawar yin bankwana da kungiyar.
Shugaban kungiyar tarayyar turai din Jean-Claude Juncker ya bayyana bukatar bude tattaunawar da Birtaniya, wacce ya ce; ficewarta daga turai din ba abu ne mai dadi ba, duk da cewa dama babu kwakkawarar alaka a tsakanin bangarorin biyu.
Juncker dai yana maida martani ne akan sanarwar da Pira ministan Birtaniya David Cameron ya yi a jiya juma'a na cewa; zai yi murabus a watan Oktoba, don haka wanda zai gaje shi ne zai bude tattaunawar sallamar juna da turai.
Shugaban tarayyar turai din dai da ya yi wata hira da tashar telbijin din kasar Jamus, ya ce; Tunda dai Mutanen Birtaniya Sun zabi ficewa daga kungiyar ta turai a ranar alhamis, to babu wani dalili da zai sa a jira har zuwa watan Oktoba domin bude tattaunawar rabuwa da juna.
Al'ummar Birtaniya dai sun kada kuri'ar ficewar daga tarayyar turai din ne a ranar alhamis din da ta gabata.