EU Ta Bukaci Biritaniya Ta Gaggauta Ficewa
-
firaministan Biritaniya David Cameron da shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel
Kungiyar tarayyar turai ta nemi kasar Biritaniya data hanzarta ficewa daga cikin kungiyar.
Shugaban majalisar turai, Martin Schulz ya bukaci firaministan Biritaniya David Cameron daya fara shirye-shiryen ficewar kasar daga kungiyar tun daga ranar Talata mai zuwa, wace kungiyar ta EU zata gudanar da taron ta.
Mr Schulz, ya ce ranar taron na EU ita ce ta dace ga kasar ta Biritaniya domin ta bayyana matsayin ta.
Kamar yadda doka mai lamba 50 na yarjejeniyar Lisbone, wace dai ba'a taba aiki da ita ba har kawo yanzu, idan Biritaniya zata aiwatar da shirin ta na ficewa to zata gabatar da anniyar ta gaban majalisar turai wace ta kunshi shugabani da gwamnatoci na kungiyar.
Bayan dai zaben al'ummar Biritaniya na ficewa daga kungiyar na ranar Alhamis data gabata firaministan kasar David Cameron ya shelanta cewa zai sauka daga mukaminsa nan da zuwa watan Oktoba, domin wanda zai gaje shi ya samu damar aiwatar da tattaunawa da kungiyar Tarayyar Turan akan ficewar Biritaniya.