An bude masallaci bayan jayayar shekaru 15 A Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i7582-an_bude_masallaci_bayan_jayayar_shekaru_15_a_faransa
An bude wani masallaci a birnin Nice da ke kudancin Faransa, bayan mahukuntan yankin sun shafe shekara 15 suna adawa da bude masallacin.
(last modified 2018-08-22T06:58:32+00:00 )
Jul 03, 2016 00:42 UTC
  • An bude masallaci bayan jayayar shekaru 15 A Faransa

An bude wani masallaci a birnin Nice da ke kudancin Faransa, bayan mahukuntan yankin sun shafe shekara 15 suna adawa da bude masallacin.

Jami'in da ke kula da yankin ne ya amince da bude masallacin, bayan magajin gari, Philippe Pradal ya bayyana asdawarsa da hakn

Shi ma magajin garin da ya gabace Philippe Pradal , wato Christian Estrosi ya yi adawa da buda masallacin sakamakon zargin da yake cewa wanda ya gina masallacin, wato Ministan harkokin wajen Saudiyya, Sheikh Saleh bin Abdulaziz yana kokari ne ya taimaka wajen kafa shara'ar musulunci, tare da murkushe dukkan Coci-coci a kasar Saudiyyar.

Wata kotu ce ta yanke hukuncin da ya ba da damar bude masallacin, wadda ta ce adawar da mahukunta ke yi da bude shi ya saba da 'yancin da kundin tsarin mulkin kasar ya bayar na bin addinin da mutum ke so.

shi dai wannan masallaci na daukan masallata 880 ne.