EgyptAir : An Sake Gano Wasu Sassan Jikin Mutane
Jul 04, 2016 00:54 UTC
Tawagar masu bincike kan musababbin faduwar jirgin nan na EgyptAir da ya fado a tekun Bahar Rum a watan Mayu sun sake gano wasu sassam jikin mutane.
Masu binciken sun ce zasu sake komawa a gurin da aka gano takarcen jirgin fasinjan kira A320 har sai sun tabbatar cewa babu sauran wasu sassan jikin mutum da aka baro.
Jirgin dai na Masar ya fadi ne a ranar 19 ga watan Mayu da ya gabata bayan tashin sa daga birnin Paris na Faransa zuwa birnin Alkahira na Masar daukeda mutane 66.
Har kawo yanzu kuma ba'a kai ga sanin musababin fadauwarsa ba.
A halin da ake ciki dai an gano dukkan akwatinan nadar bayanan tukin jirgin guda biyu wadanda zasu baiwa masu bincike damar gano musababin faduwar jirgin.
Tags