Tsanantar Hare-haren Ta'addanci A duniya.
https://parstoday.ir/ha/news/world-i7669-tsanantar_hare_haren_ta'addanci_a_duniya.
al-Mayadeen: Shan Kashin Da'esh Ne Ya Sa Su ke Tsananta Kai Hare-hare.
(last modified 2018-08-22T06:58:32+00:00 )
Jul 05, 2016 07:23 UTC
  • Tsanantar Hare-haren Ta'addanci A duniya.

al-Mayadeen: Shan Kashin Da'esh Ne Ya Sa Su ke Tsananta Kai Hare-hare.

Tashar telbijin din al-mayadeen mai watsa shirye-shiryenta da Larabci ta ce; Shan kashin da kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh, ta ke yi ne, ya sa su ke tsananta kai hare-hare a cikin kasashe.

Rahoton na al-mayadeen ya ci gaba da cewa; A cikin kasashen Iraki da Syria da Libya, Da'esh tana shan kashi abinda ya sa su ke tsananta kai hare-haren ta'addanci.

Wani sashe na rahoton ya yi ishara da cewa; ita wannan kungiyar ta Da'esh ba ta taraddudin kai hari a cikin kowace kasa, kuma basu banbanta tsakanin wata kungiya ta addini da wata kungiya.

A Cikin kasashen turai da kuma kasuwannin Iraki da Suria da Kuwaiti da Saudiyya kungiyar ta Da'esh tana kai hari ba tare da wani banbanci ba.

A cikin biranen Fallujah na Iraki da kuma Sart na Libya an fatattaki kungiyar Da'esh, yayin da a kasar syria ma su ke fuskantar matsin lamba.

A jiya litinin ne dai aka kai wani harin kunar bakin wake mai hatsarin gaske a kusa da masallacin ma'aikin Allah da ya ke a birnin Madina. Jami'an tsaron Saudiyyar sun ce 'yan sanda biyu sun kwanta dama.