Kotu ta dauke wasu tsofin 'yan ta'addar ISIS 7 a Faransa
Wata Kotu a Faransa ta yanke hukunci dauri kan wasu tsofin 'yan ta'addar ISIS 7.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a jiya Laraba Wata kotu a birnin Strasbourg da ke Faransa ta yanke hukuncin dauri na shekaru 6 zuwa 9 a gidan yari, kan wasu ‘yan asalin kasar su 7 da suka je Syria domin shiga ayyukan jihadi.
Wasu daga cikin mutanen da aka yanke wa hukuncin sun hada da wadanda suka taimaka domin kai hari a gidan rawa na Bataclan da ke Paris a watan nuwambar shekarar da ta gabata bayan dawowarsa daga Syria.
Wasu daga cikin wadanda ake yankewa wannan hukunci sun tabbatarwa kotu cewa ba su je Siriya ba saboda Addini, manufar su taimakawa kungiyar ISIS domin yakar Gwamnatin Damuscus
Hakazalika kotu ta bayar da umurnin a sanya sunayen mutane 7 a cikin jerin sunayen wadanda Faransa ke kallo a matsayin ‘yan ta’adda.
Rahoton ya ce Mutanan da ake yankewa wannan hukunci sun hade da kungiyar ISIS ne a shekarar 2013 da 2014.