Martanin Faransa kan korafin Iran
Ma'aikatar Harakokin wajen Faransa ta ce babu wata alaka tsakanin ta da kungiyar 'yan ta'adda munafikai a kan zaman da suka yi a birnin Paris
A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Laraba, Kakakin Ma'aikatar harakokin wajen Kasar Faransa Romain Nadal ya ce Gwamnatin faransa ba ta da wata alaka da kungiyar 'yan ta'addar masu adawa da Gwmanatin Iran hasali ma Faransa na kallon wani Kungiyar a matsayin masu tayar da kayar baya da ta yi hanun rika da tafarkin Democradiya.
Mista Nadal ya kara da cewa kadamar da tashe tashen hankula da ya sabawa tafarkin Democradiya na wannan kungiya da Gwamnatin Iran din ke kallon ta a matsayin kungiyar munafikai kuma 'yan ta'adda ya sanya kungiyoyin kare hakin bil-adama da dama bukatar neman kungiyar da ta dakatar da aiyukan ta na tayar da kayar baya ko kuma tayar da tayar da hankali.
A ranar Assabar din da ta gabata ce kungiyar 'yan ta'adda munafikai masu adawa da Gwamnatin Jumhoriyyar Musulinci ta Iran ta gudanar da taron ta a birnin Paris na kasar Faransa.
Ita dai wannan Kungiya Iraniyawa ne masu adawa da juyin juya halin musulinci na Iran da suka gudu kasashen waje, a farkon juyin juya halin musulincin kungiyar ita ce ke da alhakin ta'addancin da ake yiwa manya manyan masana da dubun 'yan kasar ta Iran.
Bayan gudanar da wannan zama, Gwamnatin Iran ta kira Jakadan Faransa dake nan birnin Tehran inda ta bayyana mana rashin jin dadinta da yadda aka bar wannan kungiya ta gudanar da taro a birnin Paris din, a nasa Bangare Mista Francois Senemaud Jakadan nan faransa dake nan birnin Tehran ya yi alkawarin meka wannan sako ga Magabatan Faransa.