Kasar Faransa Ta Rufe Ofishin Jakadancin Ta Dake Kasar Turkia
Faransa ta rufe ofisoshin jakadanci babban da kuma kana a kasar Turkia
Gwamnatin Kasar Faransa ta bada sanarwar rufe ofishin jakadancinta dake birnin Ankara babban birnin kasar Turkia da kuma karamin ofishin jakadancinta dake birnin Isatambul. Tashar television ta Prersstv a nan Tehran ta bayyana cewa dalilan da gwamnatin kasar Faransa ta bayar na daukar wannan matakin shi ne rashin cikekken tsaro.
A ranar 28 ga watan Yuni da ya gabata ne wasu yan ta'adda, wadanda gwamnatin kasar Turkia ta ce mayakan Daesh ne suka kai harin kunan bakin wake guda biyu a babban tashar jiragen sama na kasar da ke Istambul suka kuma bude wuta kan mutane, inda akalla mutane 41 aka tabbatar da mutuwarsu, sannan wasu daruruwa kuma suka ji rauni. Tun kafin haka ma an sha kai hare hare nan da can a kasar ta Turkia wadanda gwamnatin take aza laifin hakan a kan kungiyoyin yan ta'adda na Daesh da kuma PKK ta kurdawa.