Gurbataccen Bayani Kan Harin Ta'addanci A birnin Nice Na Kasar Faransa
Manufar kasashen yamma shi ne munana addinin musulunci a gaban mutanen kasashensu da kuma duniya gaba daya.
A ranar Alhamsi da ta gabata ce wani dan ta'adda ya tuka wata babbar mota inda ya nufi inda faransawa da baki yan kasashen waje suke gudanar da bukukuwan ranar kasar Faransa a birnin Nice na kasar Faransa, ya hau kan mutane da babbar motarsa ya kuma yi ta yin barin wuta da wata bindiga dake hannunsa a kan wasu mutane, inda kafin yan sanda su shawo kansa su kuma kashe dai ya kashe mutane akalla 84.
Kungiyar yan ta'adda ta Daesh kamar yadda ta saba ta dauki alhakin kai wannan mummun hari.
Sai dai duk tare da cewa mahaifin Muhammad Bu- Hilali dan shekara 31 a duniya wanda ya aikata wannan kisan kiyashin ya fadawa kafafen yada labarai na kasar Faransan cewa dansa ba mutum ne mai riko da addini ba, don yana shan giya yana shan kwayoyi, baya salla kuma baya azumi.
Banda haka tsohuwara matarsa ta fadawa jaridar "Daily Mail " ta kasar Britania cewa tsohon mijinta baya salla baya azumi yana cin naman alade, amma abin mamake shi kafafen yada labarai na kasashen Turai musamman na kasar Faransa suna dage wajen danganta aikin wannan matashin dan asalin kasar kasar kan cewa ya aikata abinda ya aikata ne da sunan addinin Musulunci. Suna kuma danganta ayyukan kungiyoyin yanta'adda irinsu Daesh da addanin musulunci.
Abu ne a fili yake ga duk wanda ya san tarihin manzon Al...(s) da kuma tsarkakekken addinin da ya zo da shi, kan cewa addini ne mai tausayewa hatta dabbobi bellamtana mutane. Duk wanda ya karanta tarihin musulunci ya san cewa, addinin ya yadu ne da kekyauwan halayen manzonn Al..(s) a farkon bayyanarsa. A halin yanzu kuma a duniyarmu ta yau kasar musulmi mafi girma a duniya, wato Indonasia wacce take da musulmi fiye da miliyon 200, addinin ya yadu a kasar ne ba tare da daukar takobi ba ko amfani da karfi ba.
Don haka addinin musulunci ko kadan bai amince da ayyukan ta'adda wadanda wadan nan yan ta'adda suke aikatawa da sunansa ba.
Sai dai abinda za'a iya fahinta daga irin yadda wadan nan kafafen yada Labarai na kasashen yamma suke son cimmawa da tuhumar musulmi da musulunci kan ayyukan wasu tsiraru wadanda suke dangnata kansu da addinin shi ne,cewa suna son amfani da wannan damar don takurawa musulmi wadanda suke rayuwa a kasashensu da kuma amfani da wannan damar don cimmu mummunan siyasarsu a kasashen musulmi da kuma duk inda musulmi yake rayuwa a duniya.
Idan ba haka ba, ai idan da wani kirista ne ya aikata irin ayyukan Daesh ko kuma ayyukan muhammad Bu Hilila a birnin Nice, na tabbatar bazu dorawa kiristoci da kuma addinin kirista ayyukan wannan kiristan ba. Har'ila yau muna iya fahintar cewa manufofin wadan nan kafafen yada labarai shi ne munana addinin musulunci a gaban mutanen kasashen yamma, da sauran kasashen duniya don jahiltansa da suka yi.
Daga karshe abinda ya hau kan musulmi a ko ina yake a duniya a halin yanzu shi ne tabbatar da cewa ya isarwa mutanen da basu san addinin musulunci ba ko kuma aka ruda su da wannan farfagandar, su fahintar da su asalin addinin musulunci su kuma bayyana na masu hakikanin yadda musulunci yake mutunta bi'adama ko waye shi, da kuma yadda addinin musulunci yake son zaman lafiya yake kuma kodaitar da mabiyansa da samar da shi a ko ina suke a duniya.