An Samu Karuwar Kyamar Musulmi A Kasashen Birtaniya Da Faransa
An samu karuwar kyamar mabiya addinin musluncia cikin kasashen Birtaniya da kuma faransa a cikin lokutan baya-bayan fiye dakowane lokaci a shekarun da suka gabata.
Shafin yada labarai na TRT World ya bayar da rahoton cewa, a cikin 'yan makonnin nan an samu karuwar ayyuka na nuna kyama ga mabiya addinin muslunci a cikin wasu kasashen nahiyar turai, musamman ma a Birtaniya da kuma Faransa.
Rahoton ya ce hakan baya rasa nasaba ne da hare-haren ta'addancin da aka kaddamar a cikin 'yan lokutan nan a kasashen turai daban-daban, wanda 'yan ta'addan takfiriyyah wahabiyawa masu da'awar jihadi suke kaddamarwa.
Fayyad Magul shi nhe shugaban cibiyar sanya ido kan hakkokin musulmi a kasar Birtaniya, ya bayyana cewa abin da yake faruwa a halin yanzu a kan musulmi yana ban mamaki matuka, domin kuwa suna fuskantar kiyayya mai tsanani daga wasu mutanen kasar.
Ya ce musulmi sun sha bayyana cewa abin da 'yan ta'adda suke yi ba su wakiltar musulmi balantana abin da suka yi ya shafi dukkanin musulmi, domin kuwa da dama daga cikin kasashen da aka kai harin daga cikin wadanda aka kashe har da musulmi, kuma mutanen da 'yan ta'adda suke kashewa a kullum rana idan aka kwatanta fiye da kashi casa'in musulmi ne a kasashen musulmi suke tayar da bama-bamai da kai hare-hare fiye da na turai.
Haka nan kuam ya yi ishara da cewa, kungiyoyin musulmi a dukaknin kasashen turai suna yin iyakacin kokarinsu na wayar da kan musulmi kan sahihiyar fahimta ta musulunci ba ta tsatsauran ra'yi da ta'addanci ba, kuma gwamnatocin turai sun san hakan.
A can kasar faransa ma irin cin zarafin da musulmi suke fuskanta ya karu matuka fiye da kowane lokaci a tarihin kasar musamamn ma mata da suke saka lullubia kawunansu, sakamakon kai hare-haren baya-bayan nan da wasu 'yan ta'adda suka yi.