Gwamnatin Masar Ta Dauki Alkawarin Warware Matsalolin Tattalin Arzikin Kasar
Gwamnatin Masar ta dauki alkawarin cewa da zarar ta karbi bashi a bankin bada lamuni na duniya zata fara aiwatar da gyare-gyare a harkar tattalin arzikin kasar.
A sanarwar da gwamnatin Masar ta fitar yana dauke da cewa: Da zarar kasar ta samu bashin kudade da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 12 daga Asusun bada lamuni na duniya zata fara aiwatar da gyare-gyare a harkar tattalin arzikin kasar.
Har ila yau gwamnatin Masar ta gabatar da shawara ga Majalisar Dokokin Kasar kan amincewa da shirinta na aiwatar da gyare-gyare a harkar tattalin arzikin kasar na tsawon watanni goma sha takwas.
Rahotonni sun bayyana cewa; Har zuwa yanzu akwai sabani a tsakanin gwamnatin Masar da bankin bada lamuni na duniya kan bukatar da bankin duniyan ya gabatar na rage kimar kudin kasar Masar da kuma neman jinkirta fara aiwatar da gyare-gyare a wasu bangarori masu muhimmanci da suke da alaka da tattalin arzikin kasar.