Fidel Castro Ya yi Suka ga shugaban kasar Amurka Barrack Obama.
(last modified Sun, 14 Aug 2016 14:54:01 GMT )
Aug 14, 2016 14:54 UTC
  • Fidel Castro Ya yi Suka ga shugaban kasar Amurka Barrack Obama.

Tsohon shugaban Kasar Cuba Ya Soki shugaban Kasar Amruka

Tsohon shugaban kasar Cuba, Fidel Castor ya soki Shugaba Barrack Obama na Amurka saboda kin neman gafarar al'ummar kasar Japan.

Castro wanda ya ke ishara da jefa bom din Nukiliyar da Amurka ta yi a kasar Japan,  wanda kuma ya jawo mutuwar dubban mutane, ya yi tir da kin neman gafarar al'ummar kasar da Barrack ya yi.

Tsohon shugaban na kasar Cuba, ya bayyana abinda Amurkan ta yi da cewa yana cin karo da 'yan adamtaka, sannan kuma ya bukaci ganin zaman lafiya ya samu a ko'ina a duniya.

A yayin ziyarar karshe da shugaban na kasar Amurka ya kai zuwa Japan, bai nemi gafara ba akan kisan dubban mutanen Nagasaki da Hiroshima da kasarsa ta yi a lokacin yakin duniya na biyu.

Adadin mutanen da su ka mutu dai, sun kai dubu 220 a harin na 1945.