Koma Bayan Farashin Man Fetur A Asiya
(last modified Fri, 19 Feb 2016 12:41:44 GMT )
Feb 19, 2016 12:41 UTC
  • Koma Bayan Farashin Man Fetur A Asiya

Farashin Man Fetur ya sami koma baya a nahiyar Asiya a yau juma'a.

Karuwar Man fetur na najiya a Amurka da kuma kin aincewar Saudiyya ta rage wanda ta ke fitarwa, sun kayar da farashin man fetur din kasa a kasuwannain yankin Asiya.

Cinikin man fetur din "Light Sweet" da aka yi a yau juma'a wanda kuma za a mika shi ga wadanda su ka saya a ranar 29 ga watan Maris, ya kama akan dalar Amurka 30,48 akan kowace ganga.

Har ila yau an sayar da man samfurin "Brent" akan dalar Amruka 33,98 kowace ganga.

Tun a cikin watan Yuni na 2014 ne dai aka fara samun koma bayan farashin man fetur din da kaso 70% saboda yawansa a kasuwa da kuma karancin masu nema,musamman kasar Sin wacce ake samun koma baya wajen amfani da man.

Kasashe Saudiyya da Rasha da Qatar da Venezuella sun amince da su ka yawan man fetur din da su ke fitarwa, bisa sharadin sauran manyan masu arzikin man zasu amince su yi hakan.