-
John Kerry Ya Mayar Wa Netanyahu Da Martani Kan Yarjejeniyar Shirin Nukiliya Na Iran
Feb 19, 2018 03:01Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya mayar wa firayi ministan Haramtacciyar kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu da martani kan batun yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya.
-
Kungiyar Tarayyar Turai Ta Yi Ta'aziyyar Mutanen Da Suka Rasa Rayukansu A Hadarin Jirgi A Iran
Feb 19, 2018 02:59Kungiyar tarayyar turai ta fitar da bayanin ta'ziyya dangane da rasuwar mutane 66 a wani hadarin jirgi da ya faru jiya a kasar Iran.
-
Mexico : Hadarin Jirgin Minista Ya Yi Ajalin Mutum 13
Feb 17, 2018 12:37Hukumomin shari'a a jihar Oaxaca a kudancin Mexico, sun ce mutum 13 ne suka gamu da ajalinsu a yayin da wani jirgi mai saukar ungulu na ministan cikin gida na kasar, Alfonso Navarrete, dake kan hanyar zuwa yankin da girgiza kasa ta auka ma a jiya Juma'a ya yi hadari.
-
Iran da Indiya Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyi Na Aiki Tare Guda 15
Feb 17, 2018 07:50Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Indiya sun sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi guda 15 na aiki tare a tsakanin kasashen biyu a kokarin da ake yi na karfafa alakar da ke tsakaninsu.
-
'Yan Majalisar Pakistan Sun Yi Watsi Da Shirin Gwamnatin Kasar Na Tura Sojoji Saudiyya
Feb 17, 2018 07:49'Yan majalisar dokokin kasar Pakistan sun yi watsi da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na tura sojoji zuwa kasar Saudiyya suna masu cewa hakan ya saba wa kudurin da Majalisar ta fitar da ta bukaci gwamnatin ta ci gaba da zama 'yar ba ruwanmu dangane da yakin da Saudiyyan ta kaddamar kan kasar Yemen.
-
Al'ummar Garin Afrin sun Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Adawa Da Hare-Haren Turkiya
Feb 16, 2018 02:58Duban 'yan kasar Siriya mazauna garin Afrin dake arewacin kasar sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da hare-haren da dakarun saman turkiya ke kaiwa kan al'ummar yankin.
-
Dalibi Ya Bude Wuta, Tare Da Hallaka Mutane 17 A Florida
Feb 15, 2018 02:22Rahotanni daga Amurka na cewa mutane 17 ne suka hallaka, kana wasu akalla 14 suka ji rauni, a yayin da wani tsohon dalibi ya bude wuta a wata makarantar sakandare dake jihar Florida.
-
Kasashen Duniya Sun Bada Dala Biliyan 30 Don Gina Iraki
Feb 15, 2018 02:21Kasashen duniya, sun alkawarta samar da dalar Amurka Biliyan talatin, don sake gina kasar Iraki, da yakin da aka shafe tsawon shekara uku ana yi da kungiyar 'yan ta'adda ta (IS) ya daidaita.
-
Faransa Ta Hallaka Masu Da'awar Jihadi 10 A Mali
Feb 15, 2018 02:21Majiyoyin tsaro a Mali, sun ce a kalla mayakan dake da'awar jihadi goma ne suka hallaka a wani harin sama da na kasa da sojin Faransa suka kai a arewacin Mali.
-
Faransa: Idan Amfani Da Makaman Guba A Kan Fararen Hula Ya Tabba A Kasar Siria Faransa Zata Kai Mata Hari
Feb 14, 2018 02:47Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa a duk lokacin da ya tabbata a gareshi kan cewa gwamnatin kasar Siria ta yi amfani da makaman guba kan fararen hula a kasar, gwamnatinsa zata kai hari kan wuraren da aka harhada makaman a kasar Sirya.