-
MDD: Myanmar Tana Ci Gaba Da Hana Musulman Rohingya Komawa Gida.
Feb 14, 2018 02:47Gwamnatin kasar Myanmar ta ki barin musulman Rohingya komawa gida duk tare da yerjejeniyar da tacimma da kasar Bangladesh kan hakan da kuma bukatar majalisar dinkin duniya na tayi hakan.
-
Amurka : Farmakin Turkiyya A Siriya, Ya Raunana Yaki Da IS_Tillerson
Feb 13, 2018 13:43Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya bayyana cewa farmakin da Turkiyya ke kaiwa kan mayakan Kurdawa a arewacin Siriya, ya raunana yakin da ake da kungiyar 'yan ta'adda ta IS.
-
Sabon Zargin Tawagar MDD Da Lalata A (DRC)
Feb 13, 2018 13:11Tawagar MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar demokuradiyar Congo ta karbi rahotannin wasu zarge-zargen aikata ba daidai ba, ciki har da wasu laifukan yin lalata guda uku da ake zargin ma'aikatan nata da aikatawa.
-
Kasafin Kudin Amurka Zai Kara Kawo Talauci A Kasar
Feb 13, 2018 08:52Sanatan Jahar Vermont na Amurka ya bayyana cewa kasafin kudin gwamnatin Trump shi zai kara dagula al'amuran tattalin arziki, talauci da kuma tabarbarewa tarbiya a kasar
-
Jakadan Iran A Nijeriya: Gabatar da Tsarin Demokradiyya Na Addini Na Daga Cikin Nasarorin Juyi Musulunci na Iran
Feb 12, 2018 14:28Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Nijeriya, Mortadha Rahemi, ya bayyana cewar gabatar da tsarin demokradiyya na addini daya ne daga cikin nasarori masu muhimmancin gaske da juyin juya halin Musulunci na Iran ya samu.
-
Faduwar Jirgin saman Fasinja A Kasar Rasha Ta Lashe Rayukan Mutane Fiye Da 70
Feb 11, 2018 15:48Jirgin saman fasinjan kasar Rasha ya fadi jim kadan bayan tashinsa daga filin jirgin saman Domodedovo da ke birnin Moscow fadar mulkin kasar a yau Lahadi, inda dukkanin mutanen da suke cikin jirgin fiye da 70 suka rasa rayukansu.
-
Kungiyar Kare Hakin Bil-Adama Ta Soki Masar Kan Tauye Hakkin 'Yan Adawa
Feb 10, 2018 07:47Kungiyar kare hakin bil-adama ta kasa da kasa ta yi kakkausar suka kan yadda gwamnatin kasar Masar ke ci gaba da take hakkin 'yan adawa a kasar
-
Faransa: Babu Wani Dalili Da Ke Nuna Gwamnatin Siriya Ta Yi Amfani Da Makamai Masu Guba
Feb 10, 2018 02:15Ministar tsaron kasar Faransa, Florence Parly, ta bayyana cewar har ya zuwa yanzu babu wani kwakkwaran dalili da ke tabbatar da cewa gwamnatin kasar Siriya ta yi amfani da makamai masu guba a kan 'yan tawayen kasar.
-
Dakarun Yemen Sun Tarwatsa Wata Cibiyar Makamai Masu Linzami Na Saudiyya A Ta'iz
Feb 10, 2018 02:15Dakarun kasar Yemen da suke samun goyon bayan dakarun Ansarullah na kasar sun sami nasarar tarwatsa wata cibiyar makamai masu linzami da ke karkashin kulawar sojojin haya na Saudiyya lardin Ta'izz da ke kudu maso yammacin kasar Yemen din.
-
Gasar Olympics : Samsung Ya Nemi Afuwar Iran
Feb 09, 2018 11:51Kamfanin Samsung mallakar Koriya ta Kudu ya nemi afuwa ga Iran, akan kin baiwa 'yan wasan kasar dake halartar gasar Olympics ta hunturu wayar komai da ruwanka ta musaman da akayi saboda wasannin.