MDD: Myanmar Tana Ci Gaba Da Hana Musulman Rohingya Komawa Gida.
Gwamnatin kasar Myanmar ta ki barin musulman Rohingya komawa gida duk tare da yerjejeniyar da tacimma da kasar Bangladesh kan hakan da kuma bukatar majalisar dinkin duniya na tayi hakan.
Presstv a nan Tehran ta nakalto Filippo Grandi kwamishinan yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya yana fadawa komitin tsaro na majalisar ta allon bidiyo daga birnin Vienna a jiya talata.
Grandi ya fadawa komitin babu wani abu a kasa wanda ya nuna cewa gwamnatin Myanmar zata aiwatar da alakawin da ta dauka. Banda haka har yanzun yan gudun hijira daga yankin Rokhin na kasar ta Myanmar ma suna ci gaba da kwarara zuwa kasar Bangaladesh, don kaucewa hare-haren sojojin kasar.
Kwamishinan ya kara da cewa a cikin watan Febreru da muke ciki yan gudun hijira kimani 1,500 suka isa Bangladesh. Ya kuma kara da cewa a cikin watan Maris mai zuwa ne ruwa zai fara sauka a yankin, don haka akwai barazana ga yan gudun hijira kimani dubu 100 wadanda zaune a yankunan da ake ambaliyar ruwa. Yan gudun hijira musulmi yan kabilar Rakhinga kimani 688,000 suke samun mafaka a kasar Bangladesh ya zuwa yanzu.