-
Macron Ya ce Faransa Ba Ta Yarda Da Ra'ayin Saudiyya Kan Iran Ba
Nov 11, 2017 07:35Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewar ra'ayinsa dangane da kasar Iran ya saba da ra'ayin kasar Saudiyya kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
-
Amurka Za Ta Bai Wa Haramtacciyar Kasar Isra'ila Dala Miliyan 705 Domin Ta Kera Makamai Masu Linzami.
Nov 11, 2017 03:21Kudaden da Amurkan za ta bai wa Haramtacciyar Kasar Isra'ilan suna a karkashin kasafin kudin soja da aka gabatar a gaban majalisar dokoki ta Congress ne wanda kuma ta amince da shi.
-
Miliyoyin Masoya Ahlulbaiti Na Gudanar Da Tarukan Juyayin Arba'in A Karbala
Nov 10, 2017 06:57Rahotanni daga kasar Iraki na nuni da cewa miliyoyin mabiya da masoya Ahlulbaiti (a.s) daga duk fadin duniya suna ci gaba da taruwa a birnin Karbala na kasar Irakin don gudanar da juyayin Arba'in na Imam Husain (a.s) don tunawa da cikar kwanaki 40 da kisan gillan da aka yi wa Imam Husainin da iyalai da magoya bayansa a shekara ta 61 bayan hijirar Ma'aiki (s).
-
Amurka Zata Kara Dorawa Wasu Jami'an Gwamnatin Venezuela Takunkumi.
Nov 10, 2017 02:48Ma'aikatar Kudi na kasar Amurka ta bada labarin cewa gwamnatin kasar zata bayyana wani shiri na kara dorawa wasu karin manya-manyan jami'an gwamnatin kasar Venezuela takunkumai.
-
Gwamnatin Venezuela Ta Bukaci MDD Da Kada Ta Biye wa Rawar Amurka
Nov 09, 2017 15:33Wakilin kasar ta Venezuela a Majalisar Dinkin Duniyar Rafael Ramírez ya bukaci MDD da ta kaucewa aiki da manufofin Amurka.
-
Ansarullah Ta Sha Alwashi Ci Gaba Da Kai Hari Kan Saudiya Matukar Ba Ta Daina Kai A Kan Yemen Ba
Nov 09, 2017 07:52Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta bayyana cewar matukar dai kasar Saudiyya ta ci gaba da kai wa kasar Yemen hare-haren wuce gona da irin da take kai musu da kuma ci gaba da killace kasar, to kuwa za su ci gaba da kai mata hare-hare da makamai masu linzamin da suke da su.
-
Kwamitin Tsaro Ya Bukaci Saudiyya Ta Kawo Karshen Killace Yemen
Nov 09, 2017 02:18Kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya a bukaci kawacen da Saudiyya ke jagoranta da ya kawo karshen killacewar da ya yi wa kasar Yemen dake fuskantar barazana yunwa irinta mafi muni a shekarun goma da suka gabata.
-
Amurka / Sin : Akwai Mafita A Rikicin Koriya Ta Arewa_Trump
Nov 09, 2017 01:31Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce yana da yakini akan samun mafita kan rikicin Koriya ta Arewa.
-
Kungiyar Kai Agajin Gaggauta Ta Bukaci A Bude Iyakokin Kasar Yemen Domin Shigar Da Abinci
Nov 08, 2017 14:41Kungiyar kai agajin gaggauwa ta kasa da kasa ta bukaci da a bude dukkanin iyakokin kasar yemen domin shigar da kayan abinci da magani
-
MDD Na Kara Matsin Lamba Ga Gwamnatin Myanmar Kan 'Yan Rohingya
Nov 07, 2017 11:12Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya kira gwamnatin Myanmar data kawo karshen aikin sojinta a yankin Rakhine da kuma baiwa daruruwan musulmin Rohingya dake gudun hijira a kasar Bangaladash damar komawa gida.