-
Ministocin Harkokin Waje G7, Sun Halarci Taron Adu'o'i Hiroshima
Apr 10, 2016 23:47Ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar G7 masu karfin tattalin arziki, ciki har da John Kerry, sun halarci taron tunawa da wadanda suka mutu a Hiroshima.
-
Adadin Mutanan da suka mutu sanadiyar Gobara a kasar Indiya ya haura dari
Apr 10, 2016 13:39Sakamakon tashin gobara a wurin ibada na mabiyar Addinin Hindu a kasar Indiya sama da Mutane 100 suka hallaka yayin da wasu 250 suka jikatta
-
Mahaukaciyar Gobara Ta Kashe Mutane 48 Da Raunata Daruruwa A Kudancin Indiya
Apr 09, 2016 23:50Rahotanni daga kasar Indiya sun bayyana cewar alal akalla mutane 48 sun rasa rayukansu kana wasu sama da 200 kuma sun sami raunuka sakamakon wata mahaukaciyar gobara da ta faru a kusa da garin bakin ruwan nan na Kollam da ke kudancin kasar ta Indiya.
-
Gwamnatin Belgium Ta Sanar Da Ci Gaba Da Tsaurara Matakan Tsaro A Kasar
Apr 09, 2016 23:35Firayi ministan kasar Belgium ya sanar da cewa gwamnatin kasar za ta ci gaba da tsaurara matakan tsaro da zama cikin halin ko ta kwana duk kuwa da kame wani adadi na wadanda ake zargi da hannu cikin harin ta'addancin da aka kai wa kasar kwanakin baya.
-
Brussels: Mohamed Abrini, Ya Tabbatar Cewa Shi Ne ''Mai Malafa''
Apr 09, 2016 13:41Rahotanni daga Belgium na cewa mutumin nan mai suna Mohammed Abrini da aka cafke jiya, ya tabbatar da cewa lalle shi ne "Mai Malafa", da ake zargi shi ne mutum na uku da bam dinsa ya ki tashi, a harin Brussels.
-
Koriya Ta Arewa Ta Sake Nasarar Gwajin Makami Mai Linzami
Apr 09, 2016 12:33Kasar Korea ta Arewa ta sanar Yau Asabar da cewa tayi nasarar sake harba wasu makamai masu linzami samfurin ICMB masu iya kaiwa ko'ina.
-
Guinea Conakry : An Tsaurara Matakan Tsaro A Kasar
Apr 09, 2016 06:44Jami'an tsaro a Guinea Conakry sun dauki matakin tsaurara matakan tsaro a duk fadin kasar da nufin dakile duk wani shirin kai harin ta'addanci musamman bayan hare-haren ta'addancin da aka kai kasashen Mali da Ivory Coast.
-
Zanga-Zangar Kyamar Gwamnati A Ukraine
Apr 09, 2016 00:10An gudanar da wata zanga-zanga a birnin Kiev fadar mulkin kasar Ukraine, domin sukar lamirin gwamnatin kasar kan batun cin hanci rashawa.
-
Jami'an Tsaron Belgium Sun Kama Wasu Da Ake Zargi Da Harin Ta'addancin Brussels
Apr 08, 2016 12:56Babban mai shigar da kara a kasar Belgium ya sanar da cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kame wasu mutane da ake zargi da hannu cikin harin ta'addancin da aka kai birnin Brussels a kwanakin baya.
-
Amincewar Banki Duniya wajen bayar da Bashi ga Kasar Tanzania
Apr 08, 2016 05:15Banki Duniya ya amince Baiwa Kasar Tanzaniya Bashin Dalar Amurka million 65