-
Kasashen Afrika Na Cikin ko-ta-kwana Bayan Bullar Ebola A DRC
May 22, 2017 08:49Kasashen Afrika da suka hada da Rwanda, Uganda, Ghana, Kenya da Nigeria, sun dauki tsauraran matakai a kan iyakokinsu tun bayan samun rahoton bullar annobar cutar Ebola a Jamhuriyar demokuradiyyar Congo.
-
Taron Farko Na Hukumar Yan Sanda Ta Tarayyar Afrika AFRIPOL A Algeria
May 16, 2017 01:30An bude taron hukumar yan sanda ta tarayyar Afrika AFRIPOL a takaice a birnin Algiest na kasar Algeria, tare da halattar shuwagabannin yan sanda na kasashen nahiyar Afrika da wasu kasashen duniya.
-
Najeriya Da Morocco Sun Cimma Yarjejeniyar Shimfida Bututun Gas
May 16, 2017 01:24Kasashen Morocco da Nijeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin shimfida wani muhimmin bututun iskar gas da zai hada kasashen yammacin Afrika.
-
Ivory Coast : Gwamnati Ta Sanar Da Cimma Yarjejeniya Da Sojoji Masu Bore
May 16, 2017 01:17Gwamnatin Ivory Coast ta sanar da cimma wata yarjejeniya da sojoji masu bore, saidai ba tare da yin karin haske ba.
-
Sudan Ta Kudu : Kiir Ya Bukaci A Kwantar Da Hankali Bayan Korar Hafsan Soji
May 12, 2017 11:17Shugaban Salva Kiir na Sudan ta kudu ya yi kira ga jama'ar kasarsa da su kwantar da hankali don kuwa babu abun damuwa bayan da ya sallami babban hafsan sojin kasar Paul Malong.
-
An Samu Bullar Anobar Ebola A DR. Congo
May 12, 2017 10:45Hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da bullar annobar cutar Ebola a arewa maso gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
-
An Fara Taron Tattaunawa Ta Kasa Don Magance Rikicin Kasar Gabon
May 11, 2017 01:20An bude taron tattauna ta kasa a kasar Gabon da nufin kawo karshen rikicin siyasa da ya kunno kai a kasar to sai dai har ya zuwa yanzu shugaban 'yan adawan kasar Jean Ping yana ci gaba da kaurace wa taron.
-
Sama Da Mutane 100 Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Iskar Gas A Ghana
May 11, 2017 01:20Rahotanni daga kasar Ghana sun bayyana cewar sama da mutane 100 sun sami raunuka wasu daga cikinsu suna cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai sakamakon fashewar wata tankar daukar iskar gas a wani kamfani da ke yammacin kasar.
-
Mabiya Addinai Na Gudanar Da Tattaunawa A Kasar Morocco
May 10, 2017 14:52An fara gudanar da zaman tattaunawar addinai na kasa da kasa a birnin Hamra na kasar Morocco.
-
UNICEF: Har Yanzu Cutar AIDS Ta Kasance Barazana Ga Duniya
May 07, 2017 13:44Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewar har ya zuwa yanzu cutar AIDS ta zamanto babbar barazana ga al'ummomin duniya sakamakon ci gaba da daukar rayukan al'umma da cutar take yi.