An Samu Bullar Anobar Ebola A DR. Congo
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da bullar annobar cutar Ebola a arewa maso gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
Tuni dai annobar mai haddasa zazzabi mai tsanani da zubar da jini ta kashe mutum uku, bayan bullarta a karshen watan Afrilu da ya gabata a gandun dajin Bas-Uwele dake iyaka da Afrika ta tsakiya.
Da yake tabbatar da hakan ministan lafiya na kasar Oly Ilunga ya kira jama'ar kasar da kada su tada hankali, don kuwa gwamnati ta dauki duk matakan da suka dace don tunkarar annobar.
Hukumar WHO ta ce tana aiki kafada da kafada da hukumomin kasar domin aikewa da kayan aiki na kariya da kuma jami'ai domin shawo kan cutar wacce ta bulla a yanki mai wahalar shiga.
A shekara 2014 data gabata mutane 49 ne annobar Ebola ta hallaka a wannan kasar ta RD. Congo.