UNICEF: Har Yanzu Cutar AIDS Ta Kasance Barazana Ga Duniya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20162-unicef_har_yanzu_cutar_aids_ta_kasance_barazana_ga_duniya
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewar har ya zuwa yanzu cutar AIDS ta zamanto babbar barazana ga al'ummomin duniya sakamakon ci gaba da daukar rayukan al'umma da cutar take yi.
(last modified 2018-08-22T07:00:04+00:00 )
May 07, 2017 13:44 UTC
  • UNICEF: Har Yanzu Cutar AIDS Ta Kasance Barazana Ga Duniya

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewar har ya zuwa yanzu cutar AIDS ta zamanto babbar barazana ga al'ummomin duniya sakamakon ci gaba da daukar rayukan al'umma da cutar take yi.

Cikin wani rahoto da ya watsa a yau din nan gidan talabijin din France24 ya bayyana cewar hukumar ta UNICEF ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a yau din nan Lahadi a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan ranar "Marayu Cutar AIDS" ta duniya inda ta nuna damuwarta dangane da irin yadda kananan yara suke ci gaba da shiga mawuyacin hali sakamakon rasa iyayensu da suke yi musamman a Yammacin Afirka.

UNICEF ta ce cikin kananan yara biyar a yammacin Afirkan, guda daga cikinsu ya rasa daya daga cikin iyayensa sakamakon kamuwa da cutar ta AIDS.

Wasu rahotannin sun ce a kowane mako kimanin kananan yara dubu uku ne suke mutuwa sakamakon cutar ta AIDS, kamar yadda kuma kimanin jarirai dubu hudu ne da suke da cutar ta AIDS a jikinsu ake haihuwarsu a duk fadin duniya.