Najeriya Da Morocco Sun Cimma Yarjejeniyar Shimfida Bututun Gas
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20428-najeriya_da_morocco_sun_cimma_yarjejeniyar_shimfida_bututun_gas
Kasashen Morocco da Nijeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin shimfida wani muhimmin bututun iskar gas da zai hada kasashen yammacin Afrika.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
May 16, 2017 01:24 UTC
  • Shugaba Buhari da Sarki Mohammed na Marocco a ziyarar da ya kai Abuja a cikin 2016
    Shugaba Buhari da Sarki Mohammed na Marocco a ziyarar da ya kai Abuja a cikin 2016

Kasashen Morocco da Nijeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin shimfida wani muhimmin bututun iskar gas da zai hada kasashen yammacin Afrika.

A watan Disamban bara ne, lokacin da sarki Mohammed na shida ya ziyarci Nijeriya ne aka cimma yarjejeniyar da aka yi wa lakabi da The gazoduc atlantique, wanda zai ratsa ta kasashen yammacin Afrika, kuma mai yuwa ya dangana zuwa Turai.

Da yake gabatar da aikin a Jiya Litini ministan harkokin wajen Morocco Nasser Bourita ya ce, shimfida bututun zai yi tasiri matuka kan mutane sama da miliyan 300.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama ya jadadda cewa, kammala cimma yarjejeniyar alama ce dake nuna nasarar dangantaka dake tsakanin Rabat da Abuja.

A bisa yajejeniyar da kamfanonin kasashen biyu (NNPC) da Najeriya da (ONHYM) na Marocco sukka cimma ana hasashen kammala aikin a cikin shekara guda.